By Abbas Yakubu Yaura
Masu ruwa da tsaki a jihar Binuwai na kungiyoyin al’adu guda uku da suka hada da Mdzoungh U Tiv da Ochitoha’K’idoma da Omin’Igede da kuma wasu shugabannin kananan hukumomin jihar a ranar Litinin din da ta gabata sun koka kan sabbin dabarun da makiyaya ke amfani dasu wajen kai hare-hare kan al’umma a cikin jihar.
A wani taron manema labarai daya kira a garin Makurdi, kakakin masu ruwa da tsaki, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Ukum, Steve Ayua, yace a yanzu makiyayan dake dauke da makamai sun tsallaka magudanar ruwan kogin Binuwai da sauran magudanun ruwa domin isa yankunan da suke so.
Sannan yace lokacin noman rani ke kara gabatowa a lokutan kakar bana da makiyayan dake dauke da makamai suke tururuwa zuwa cikin jihar yana kara tada zaune tsaye.
Ayua ya kara da cewa, kananan hukumomi 21 daga cikin 23 na da tatsuniyoyi masu daci dangane da makiyayan dake dauke da makamai, inda yace basu zo da shanu ba, sai AK-47 don kashewa da raunatawa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa idan zaku iya tunawa da kisan da aka yi a ranar Asabar din data gabata, inda makiyaya dauke da makamai suka kashe mutane hudu masu gudanar da zaman makoki a Adigi dake gundumar Mbatyatyor na karamar hukumar Logo a jihar.
Kazalika “Suna harbi kan wadanda ke yunkurin kama su. Haka kuma sun dauki dabarar ‘yan daba na zuwa da daddare domin su karkashe jama’ar mu su gudu ba tare da sun fuskanci kalu-bale ba.
“Wani al’amari mai tayar da hankali da makiyayan suka bullo da shi a baya-bayan nan shi ne na zuwa mashigar ruwa a kogin Benue da sauran magudanan ruwa a cikin jihar tare da tilasta wa matuka kwale-kwale su yi jigilar su zuwa wuraren da suka nufa.inda Duk wanda yanuna turjiya daga masu aikin kwale-kwalen yana fuskantar mutuwa nan take,” in ji Ayua.
Comments 1