By Abbas Yakubu Yaura
Mazauna karamar hukumar Karim Lamido dake jihar Taraba sun yi zargin cewa karamar hukumar na cikin wani hali na zagayewar da wasu makiyaya sukayi dauke da makamai, wadanda ke hana manoma girbe amfanin gonakinsu.
Wani manomin yankin Mista Audu Jen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, a makonni biyu da suka gabata, makiyaya dauke da makamai sun mamaye al’ummomi da dama a yanki lamarin da ya tilasta wa manoma barin gonakinsu.
Shima wani mazaunin garin Musa Ibrahim ya yi zargin cewa makiyayan da suka yi hijira sun kashe mutane da dama a gonakinsu.“Ba ka kuskura kaje gona a kwanakin nan, musamman wadanda gonakinsu ke bakin kogin Benue da kan iyakar jihar Filato.
“Makiyaya sun kashe mutane da ba a tantance adadinsu ba kuma babu wanda ya sake komawa gona,” in ji Audu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban karamar hukumar, Mista Markus Hamidu, yace an kashe mutane biyu a ranar Talata a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a yankin Gwomu dake karamar hukumar.A cewarsa, wasu manoma biyu suna zuwa gonakinsu, sai suka ga wasu garken shanu suna kiwo a ciki, kuma yayin da suke zanga-zangar, sai suka far musu.
“Makiyayan sun far wa manoman inda suka kashe daya daga cikinsu. A wani harin ramuwar gayya,inda manomi daya ya kashe wani makiyayi a cikin lamarin, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa biyu.“Na yi magana da jami’in ‘yan sandan shiyya na Karim Lamido, kuma an kai gawarwakin domin binne su,” inji shi.
Sai dai wakilinmu ya tattaro daga majiyoyin cewa mutane 15 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a harin wanda ya afku a ranar Talata.
Shugaban yace, “Nan da nan muka samu labarin harin, kuma mun kai rahoto ga gwamnan wanda shi kuma ya tara jami’an tsaro wadanda har yanzu suke cikin al’ummomin da abin ya shafa.