Dayawa daga cikin malamai da wasu ma’aikatan kananan hukumomi dake Jahar kwara sun cigaba da shagali bayan gwamnan Jahar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bada umarnin kara masu girma. Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Wannan ya biyo bayan shekaru da dama da ma’aikatan suka share suna neman hakan amma basu samu ba sai wannan karon.
Shugaban hukumar ta SUBEB Farfesa Shehu Raheem Adaramaja, yake sanar da haka lokacin da yake rabawa ma’aikatan mashina, da naurar zamani da kayan koyarwa na zamani a makarantun dake Jahar ta Kwara.
KARANTA:- Dalilinmu na barin DIGs, AIGs bayan mun nada IGP, gwamnatin tarayya ta fadi dalili
Yawancin malaman kananan hukumomi dake Jahar Kwara rabonsu da samin karin girma tun shekarar 2017.
Kamar yadda Adaramaja, ya bayyana ” Tsarin Jarabawa da za’a gudanar tun daga 2017, 2018, 2019 da 2020 zai kama 2-5, ga watan Agusta 2021, kamar yadda gwamna ya amince dashi.”
“Haka kuma sauran bashin da Malamai ke bi ba’a manta da su ba, muna godiya matuka ga mai girma gwamna kan amsa kukanmu da yayi.” Kamar yadda ya fadi.
Gwamnan Jahar Kwara, wanda mataimakinsa Kayode Alabiya ya wakilce shi yace, “wannan wata hanya ce ta zaburar da Malamai da sauran ma’aikata don gudanar da ayyukan dake kansu, don ciyar da Jahar gaba.
Shugaban kungiyar Malamai ta Jahar kwamred Olu Adewara, ya nuna godiyarsa matuka ga gwamna, sannan yayi kira ga gwamna da yayi kokarin ya biya sauran bashin da ma’aikatan ke bi kamin a kara masu girma.
Abun burgewa akan karin matsayi na (2017, 2018, 2019 da 2020), shine irin fahimtar da gwamnati take dashi tsakanin ta da maaikatanta.
Daga cikin ayyukan da mai girma gwamnan ya kaddamar sun hada da samar da motoci masu daukan mutane sha takwas, Hilux kirar 2020 guda biyar, mashina Bajaj guda arba’in da biyar, wayoyi Samsung guda arba’in, naura mai kwakwalwa guda goma, kilipa guda ashirin, kayayyaki koyar da karatu daban-daban da sauran kayayyaki daban-daban.