Kungiyar Malaman Jami’o’i ta shirya gudanar da zanga-zangar kwana guda a fadin kasar nan.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ASUU za ta yi zanga zangar ne domin nuna rashin amincewa da yadda Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da shirin “ba aiki, babu biya” ga malaman jami’o’in kasar nan.
KARANTA ANAN: Dubban Magoya Bayan Jam’iyyun APC, Da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Taraba
Za a gudanar da zanga-zangar ne a matakan reshen kungiyar da ke fadin cibiyoyin jami’o’in gwamnati a fadin kasar, kuma za a yi ta ne a matsayin rana ta kyauta ga dukkan malaman da suke mambobi.
Wani mamba a majalisar zartaswar kungiyar na kasa ya tabbatar da hakan a wata da jaridar Punch, a ranar Lahadi.
Da yake tabbatar da hakan, a wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ASUU, reshen jami’ar Legas, Dakta Dele Ashir, ta bayyana cewa reshen zai gudanar da zanga-zanga a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba, 2022.
Wasikar wacce aka aika zuwa ga “dukkan masu ruwa da tsaki” ta lura cewa taron zanga-zangar na adawa ne da cin mutuncin tunani a Najeriya, kuma zai gudana ne a ranar Talata, 15 ga Nuwamba, 2022, a dakin taro na Julius Berger.
Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya kasa jin ta bakinsa domin jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin kuma: Ma’aikatan Gwamnati Sun Koka Kan Zirarewar Albashin Su Wajen Siyen Fetur
Comments 1