Tsohon sakataren NNPP na shiyya kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Sanata Rabiu Kwankwaso, Dr Babayo Liman da shugabannin kananan hukumomi 17 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar yobe.
Sun bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da tsohon sakataren jam’iyyar NNPP na shiyyar da sauran wadanda suka sauya sheka suka yi wa manema labarai karin haske a sakatariyar NUJ da ke Damaturu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Karbar Katin Zabe: INEC Ta Yi Kakkausan Gargadi ga Ma’aikatan Ta Kan Karbar Cin Hanci
Babayo Liman ya ce sun kasance a sakatariyar NUJ domin sanar da jama’a cewa ya yi murabus daga mukaminsa na mamba a kwamitin yakin neman zabe ya koma jam’iyyar PDP domin marawa dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar baya.
Ya ce akwai shugabannin NNPP na kasa guda biyar da suka koma PDP a yankin Arewa maso Gabas.
Liman ya bayyana cewa wadanda suka koma PDP sune; Alhaji Shehu Barau ma’ajin kasa daga Bauchi, Hajiya Halima Tafawa Balewa, shugabar mata ta shiyyar ta kasa, da jami’ar hulda da jama’a na shiyyar a karkashin NNPP da Ibrahim Tal sakataren jam’iyyar na kasa na shiyyar.
“NNPP ba ta da wani tsari kwata-kwata. Me za su kawo wa ’yan Najeriya, Jam’iyyar NNPP ta samu matsala a Bauchi wadda ta shafe sama da watanni 5 ba tare da an warware ta ba. Don haka idan Sanata Rabi’u Kwankwaso ba zai iya magance wata matsala a wata jam’iyya cikin watanni 5 ba, ba mu ga dalilin da zai sa ba za mu iya ficewa daga jam’iyyar ba.
“Da farko muna da matsalolin rashin tsaro a Najeriya wanda ya shafi yawancin jihohin Arewa maso Gabas a lokacin gwamnatin PDP kuma sun yi duk mai yiwuwa don ganin ba ta ta’azzara ba.
“Muna fatan idan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya zai yi irin abin da PDP ta yi a shekarun baya,” in ji shi
A wani labarin kuma, Jami’ar BUK Ta Musanta Kara Kudin Makaranta Ga Dalibai
Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta musanta labarin dake yawo gari cewa ta kara kudin makaranta g daliban dake karatu a cikin da wadanda ke son shiga.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Jami’ar Lamara Garba, in da ya ce labarin ba gaskiya bane.