Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta musanta labarin dake yawo gari cewa ta kara kudin makaranta g daliban dake karatu a cikin da wadanda ke son shiga.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Jami’ar Lamara Garba, in da ya ce labarin ba gaskiya bane.
KU KARANTA: Everton Na Son Daukar Wayne Rooney Bayan Korar Lampard
Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, wadda aka wallafa a mujallar Jami’ar, ya bukaci iyayen dalibai, da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulan su.
Sanarwar ta kara da cewa jami’ar har yanzu bata gama tsayar da matsaya ba kan, kudin makaranta da ya kamata dalibai su biya a bana.
Yanzu haka dai jami’o’i musamman na gwamnatin tarayya na ci gaba da kara kudin makaranta ga dalibai.
Lamarin da ke haifar da damuwa ga daliban da iyayen su, suna masu neman da a sassauta.
A wani labarin kuma: Hukumar NYSC Da CBN Zasu Hada Kai Wajen Amfani Da Tsarin E-Naira
Hukumar masu yiwa kasa hidima, NYSC, na shirin gabatar da E-Naira ga duk yan kasar nan dake cikin shirin.
Hukumar NYSC za ta hada gwiwa da babban bankin kasa, CBN kan yadda ake amfani da kudin yanar gizo ga mambobin kungiyar.
Tsarin zai saukaka wajen biyan kuɗi ba tare da haɗari ko fargaba ba.