Man United na Neman wasu zaratan Ƴan Wasa, a ƙoƙarin ta na inganta Ƙungiyar
Man United ta kara sanya sunayen wasu a jerin ‘yan wasan da ake nema yayin da mai horaswa Ten Hag ke ƙoƙarin inganta ƙungiyar.
Ƙungiyar ta Manchester United na ci gaba da neman Jarrad Branthwaite na Everton da kuma Jean Clair Todibo na Nice yayin da kungiyar ke neman ƙara karfafa bayan ta karkashin kocinta Erik ten Hag.
Man United ta samu kanta a matsayi na bakwai a teburin gasar Premier bayan da ta yi rashin nasarori a gasar a karkashin Ten Hag.
Haka ma kungiyar ta Red Devils an yi waje da ita daga gasar zakarun Turai inda ta ƙare a matakin ƙarshe na rukuni a watan da ya gabata.
A cewar Jaridar Evening Standard Man United za ta ba da fifiko wajen siyan dan wasan gaba mai buga lamba 9 mai gogewa irinta ɗan wasan Bayern Munich Harry Kane, don tallafawa Rasmus Hojlund wanda ya ci kwallaye biyu kacal tun ya koma Old Trafford da buga wasa daga Ƙungiyar Atalanta.
KARANTA WANNAN LABARIN:Jami’a ta ɗage ranar da za a cigaba da Zangon karatu saboda zanga-zangar Ɗalibai
Rahoton ya kara da cewa Man United kuma tana sha’awar kawo karin wani ɗan wasa mai gogewa mai buga lamba 8 domin karfafa tsakiyar, da kuma ɗan wasa mai buga baya a tsakiya.
An yi iƙirarin cewa an ƙara Branthwaite da Todibo cikin jerin zaɓaɓɓun ƴan wasa waɗanda Man United ke nema a masu buga baya.
Kungiyar ƙarƙashin Ten Hag tana sa ran za ta fuskanci gasa mai tsanani wajen neman ‘yan wasan biyu, wanda ke nuna cewa wataƙil su matsa lamba, ko kuma su hakura zuwa wata sabuwar kakar wasan.
A wani labarin kuma:Kada ka kuskura ka tsaya takarar shugaban kasa a 2027’ – PDP ga Atiku
Kada ka kuskura ka tsaya takarar shugaban kasa a 2027’ – PDP ga Atiku
Wata kungiya mai matsa lamba a cikin jam’iyyar PDP, wato Concerned PDP League, CPDPL, ta yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, da kada ya sake tsayawa takara a 2027.
Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Lahadi kuma ta fitar a Abuja ta hannun sakatarenta na kasa, Alhaji Tasiu Muhammed da kuma mukaddashin daraktan yada labarai da sadarwa na kasa, Gbenga Adedamola.