Jami’a ta ɗage ranar da za a cigaba da Zangon karatu saboda zanga-zangar Ɗalibai
Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Akure FUTA ta dage ranar da za ta ci gaba da gudanar da zangon karatu saboda zanga-zangar da ɗalibai ke yi, ta umarci dalibai da su bar ɗakunan kwanan su.
Biyo bayan zanga-zangar da ɗaliban suka gudanar a Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Akure FUTA hukumar gudanarwar makarantar ta dage karatun dalibai na shekarar 2023/2024 har zuwa wani lokaci nan gaba.
Makarantar ta kuma umurci dukkan ɗaliban da ke cikin harabar jami’a da kuma na dakunan kwanan dalibai da su bar makarantar cikin sa’o’i 24.
Hukumar ta Jami’ar ta ba da umarnin a cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na makarantar Adegbenro Adebanjo ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ranar tunawa da mazan jiya: Ku Inganta jin dadin jami’an soji – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ga FG
Hukumar ta kuma ba da umarnin a dakatar da rajistar daliban da suka dawo da kuma biyan kudaden sabon karatun ta hanyar manhajar jami’ar da aka shirya farawa ranar Litinin 15 ga Janairu 2024.
Yana da mahimmanci a san cewa Jami’ar ba ta buɗe yin rajistar Dalibai masu dawowa ba da kuma na sabon Zango, inda a halin yanzu ta tsaida al’amurran baki ɗaya sai zuwa wani lokaci.
A kan ƙarin kudaden makaranta kuwa, jami’ar ta bada sanarwar cewa, hakan ya zama wajibi duba da tattalin arziki yayi ƙasa, akwai buƙata ɓullo da wasu tsare-tsare domin gudanar da Jami’ar yadda ya kamata.
Don tabbatar da tafiyar da jami’ar yadda ya kamata, akwai wasu sabbin tsare-tsare da ake buƙata, don haka dole tsarin biyan kuɗaɗen makaranta ya chanja, duba da yadda ya zama wajibi ga makarantar da ta kula da wutar lantarkin dakunan kwanan dalibai da tsaftacewa, da sauran su.
Yana da mahimmanci a lura cewa Karatun na matsayin kyauta ne ga duk ɗalibai, kuma ba a cajin wasu kuɗi a zaman kuɗin makaranta face kuɗin gudanarwa.