Jami’an tsaron ‘yan sanda sun cafke wani mutum mai suna Isiaka Ayobami dake gida mai lamba 2, a Ayo Ijaiye Street, dake Isheri a garin Legas, bisa kwatar wata jaririya ‘yar shekara daya wato Aishat Isiaka daga hannun mahaifiyarta wacce hakan ya janyo ta fadi kasa ta buga kai.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Bala Elkana, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya tabbatar da cewa; nan take kan yarinyar ya fashe ta kuma mutu nan take a wurin.
Elkana ya ce mahaifin jairiyar, Alhaji Garuba Isiaka, dake gida mai lamba 7, Ayo Ijaiye Street, shi ne ya shigar da rahoto ga ‘yan sanda dake ofishin Isheri dangane da lamarin.
Wanda ake zargin wadansu fustattun matasan sun kusan kashe shi a inda lamarin ya faru, inda ‘yan sanda suka ceci shi.
Rundunar ‘yan sanda sun ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da shi gaban kotu bisa zargin kisan kai.