Manomi Ya Nutse a Ruwa, Yayin da Mutane 8 Suka tsira a Hatsarin Kwale-kwale
Wani bala’i ya afku a ranar Lahadi a unguwar Kabala Doki da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, yayin da wani manomi ya nutse a ruwa tare da wasu mutum takwas da suka tsira daga hatsarin kwale-kwale a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Matasan Najeriya na son Tinubu ya zama Shugaban Ƙasa – APC
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Lahadi inda wanda abin ya shafa, mai suna Umar, ya taka kwale-kwalen domin taimakawa mutanen da suka makale a gefen kogin amma kwale-kwalen ya kife.
Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Murtala Kabala ya shaida wa Daily Trust cewa wanda ya mutum ya shahara a tsakanin al’umma kuma yana da wata gona da ke kusa da kogin.
“Abin damuwa ne saboda Umar ya san yin iyo kuma ya kasance a bakin kogi tsawon shekaru yana noma. Wannan ne ya sa muka yi mamakin samun labarin cewa ya nutse a cikin kogi daya a lokacin da yake kokarin ceto mutanen da suka makale a wancan gefen kogin. Allah ya gafarta masa kurakuransa,” inji shi.
An fahimci cewa Umar ne kawai ya nutse; sauran da ke cikin jirgin sun tsira.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Muktar Baloni, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa har yanzu ba a gano gawarsa ba.
Ya koka da yadda wani bangare na karamar hukumar ya samu ambaliya, yana mai cewa Ƙaramar Hukumar tana cigaba da tattara bayanai na gidajen da abin ya shafa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
A wani labarin kuma: Jana’izar Sarauniya Elizabeth ta nuna Ƴan Uwantaka a Tsakanin Al’umma, Ƙasashe – Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa haduwar shugabanni daga sassa daban-daban na duniya domin murnar rayuwar marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu da kuma halartar jana’izar ta, wani yunkuri ne na nuna hadin kai da jin dadin jama’a daga sassan duniya.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a birnin Landan yayin da yake tattaunawa da Manema Labarai bayan halartar jana’izar marigayiya Sarauniyar Ingila a Westminster Abbey.