By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu masu kaifin kishin Islama su 22 saboda hare-hare 54 da suka hada da yunkurin kashe wani tsohon ministan cikin gida, kamar yadda wata majiya ta shari’a ta shaida wa AFP.
An samu mutanen da laifin aikata “ayyukan ta’addanci” guda 54 a fadin kasar Masar, ciki har da kisan wani babban jami’in ‘yan sanda da kuma yunkurin kashe tsohon ministan cikin gida Mohamed Ibrahim.Ana dai aiwatar da hukuncin kisa a Masar kan fararen hula ta hanyar rataya. Wadanda aka yanke wa hukuncin kisa sun hada da wani tsohon dan sanda, kuma ba za a iya daukaka kara kan hukuncin ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Mutanen 22 da aka yankewa hukuncin, an same su da laifin kasancewa mambobin kungiyar Ansar Beit al-Maqdis, wacce ta yi mubaya’a ga kungiyar IS a shekarar 2014.
Babbar kotun daukaka kara a kasar Masar, ta amince da hukuncin daurin wasu mutane 118 a cikin wannan shari’a, daga shekaru masu yawa zuwa daurin rai da rai.
Kasar Masar dai ta shafe shekaru tana gwabza kazamin fada a arewacin Sinai wanda ya barke bayan hambarar da shugaba Mohamed Morsi da sojoji suka yi a shekara ta 2013.A watan Fabrairun shekarar 2018, sojoji da ‘yan sanda sun kaddamar da farmaki a fadin kasar kan mayakan da suka mayar da hankali kan Arewacin Sinai.
Kimanin mutane 1,073 da ake zargin ‘yan bindiga ne da kuma jami’an tsaro da dama ne aka kashe tun bayan fara gudanar da ayyukan kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.A farkon wannan wata ne Masar ta amince da Isra’ila kan kara yawan dakarunta a kusa da garin Rafah da ke kan iyaka domin murkushe mayakan IS.
Kazalika kasar Masar, wacce ita ce kasa mafi yawan al’umma ta Larabawa, ta kasance kasa ta uku mafi yawan aiwatar da kisa a duniya – bayan China da Iran a cewar Amnesty International. A cikin shekarar 2020, hukumomin Masar sun kashe akalla mutane 107, in ji Amnesty.