Masari ya bada tallafin Miliyan 1 ga Iyalan Sojin Ƴan bindiga suka kashe a harin Magamar Jibia
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da tallafin kudi naira Miliyan Daya ga Iyalan Soja da ya rasa ransa a lokacin da Ƴan bindiga suka kai farmaki a garin Magama ta Ƙaramar Hukumar Jibia.
Baban Sakataren Tsaro Alhaji Suleiman Yakubu Safana ne ya mika gudummuwar a lokacin da ya jagoranci wani kwamiti domin yin ta’aziya ga iyalan Sojan da ya rasa ransa tare da duba wani sojan wanda ya samu rauni a yayin harin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin APCn Sokoto: Kotu ta ɗage Shari’ar har sai Baba ta gani
Bugu da kari, wannan Kwamiti ya mika gudummuwar naira 250,000 ga sojan da ya samu rauni a yayin harin domin sauƙaƙa mashi wurin biyan kuɗin magani da kuma kula da iyalansa.
Kwamandan Birget ta 17 da ke Katsina wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikata na Birget din, ya nuna godiya akan wannan karamci da Gwamnan ya yi.
Idan dai masu bibiyar Shafin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta The Fact 24 basu manta ba Ƴan bindiga ɗauke da manyan makamai sun farmaki garin Magamar Jibia a makwanni biyu da suka gabata, inda suka hallaka baturen ƴan sanda na Jibia tare da Sojan.