Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana a ranar Laraba cewa mayakan jihadi sun kashe sojojin kasar 5 a yankin tafkin Chadi, wani yanki mai fadin gaske da ya zama matattara ga ‘yan tawaye masu kishin Islama.
“Wannan rashi na baya-bayan nan, wanda za a iya danganta shi da harin ta’addanci na kungiyar Boko Haram, tunatarwa ce kan kalubalen tsaro da ta’addancin da muke fuskanta,” in ji Deby a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook.
An kai harin ne a ranar Talata a Kaiga Kindjiria, kimanin kilomita 150 (mil 95), a arewa da N’Djamena babban birnin kasar, in ji shi.
Sai dai bai bayar da karin bayani kan lamarin ba, haka ma jami’an yankin da AFP ta tuntubi.
“Jinin da suka zubar na sojojinmu ba zai zama a banza ba. Za mu ci nasara a wannan yaki da mahaukatan Boko Haram,” in ji Deby.
Kasar Chadi dai ta shafe shekaru tana yaki da masu jihadi daga makwabciyarta Najeriya. ana kiran ‘yan tawayen da sunan Boko Haram, duk da cewa kungiyar mai dimbin tarihi ta balle, inda aka samu wani bangaren da ke goyon bayan kungiyar IS.
Akalla sojojin Chadi 26 ne aka kashe a watan Agustan da ya gabata a yankin tafkin Chadi kusa da kan iyakar kasar da Kamaru.
Janar Deby mai shekaru 37 a duniya ya hau karagar mulki a watan Afrilun da ya gabata a karkashin gwamnatin mulkin soji bayan mutuwar mahaifinsa tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno sakamakon raunukan da ya samu yayin yakar ‘yan tawaye a arewacin kasar.