By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun cafke mawakan Zinoleesky da Mohbad bayan wani samame da suka kai da tsakar dare a gidan su da ke Legas.
Kakakin Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya tabbatar da hakan, ya ce jami’an sun kwato tabar wiwi da Molly.
“Mutanenmu sun kai samame a wani yanki a Idado inda yaran Kasuwar Bìara suka sauka.
An samo wasu adadin tabar wiwi da Molly daga gidansu da motarsu, ”.
“An kama mutane shida baki daya. Mata biyu maza hudu a yayin simamen.”
Wannan na zuwa ne makonni bayan da Hukumar ta kama wani makerin skit, De General, bayan wani samame da suka kai gidansa da ke Legas.
Nan take aka gurfanar da De General a gaban kotu inda aka same shi da laifin safarar tramadol da tabar wiwi.
Sai dai kotun ta yi afuwa ga mai yin skit saboda yawan magungunan da aka same shi ya yi kadan ba za a iya yanke masa hukunci ba.
Comments 1