Daga: Abbas Yakubu Yaura
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC reshen jihar Kano sun bukaci manyan shugabannin jam’iyyar da su bullo da dabarun sasanta ‘ya’yan jam’iyyar domin kwantar da hankulan su gabanin gudanar da babban zaben 2023.
Masu ruwa da tsakin sun yi wannan roko ne a lokacin da jami’an shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar, Salihu Lukman, suka gudanar da wata ganawa da su a yayin wata ziyarar gani da ido.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/sakaci-ne-ya-haddasa-harin-gidan-yarin-kuje-pdp/
Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na shiyyar Malam Musa Mailafiya Mada ya fitar a ranar Laraba ya ce hadin kan jam’iyyar ya dauki nauyi a wajen taron.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Masu halartar taron sun jaddada bukatar samar da wani shiri na sasantawa da zai magance korafe-korafen da suka biyo bayan zaben fidda gwanin da wasu daga cikin ‘yan takarar da suka ji an bata musu rai ta wata hanya ba.
“Malam Salihu Lukman ya bayyana wa mahalarta taron wasu matakan da aka sanya a matakin shiyya don tabbatar da hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma rawar da shugabanci a matakai daban-daban ke takawa wajen ganin an samu hadin kai tare da dorewarsa.”
A cewar sanarwar, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar ya nuna jin dadinsa da yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar a matakin shiyya.
A wani labarin kuma Harin da aka kaiwa gidan yarin Kuje, Abuja a Babban Birnin Tarayya Abuja an zarge shi da rashin Kyakkyawan Shugabanci na Jam’iyyar APC Mai mulki.
Da yake jawabi ga Manema labaru a Sakatariyar Jam’iyar PDP Abuja a ranar Laraba, Mataimakin Shugaban matasa Hon. Tim Osadolor yace abinda ke faruwa yanzu a Najeriya ya nuna cewa akwai rashin iya Mulkin Gwamnatin Buhari.
Osadolor wanda yana maida jawabi ga Tambayoyi daga Ƴan Jarida yace “bana addu’a ko jin haushi a Najeriya. Muna da ƴan Najeriya da suka cancanta, amma wadanda suke sun gaji sune ke mulki a wannan Gwamnatin.
“Najeriya tana ƙwararrun Sojoji masu riƙe da bayanan sirri, da sauran Jami’an tsaro, amma mutum zai tambaya.