Daga: Abbas Yakubu Yaura
Misis Yetunde Adeyanju, kwamishiniyar ma’aikatar tsare-tsare da raya birane ta jihar Ondo, ta yi murabus daga mukaminta a gwamnatin gwamna Oluwarotimi Akeredolu.
Bayan da aka dauke ta a ranar Litinin daga ma’aikatar ruwa da tsaftar muhalli zuwa ma’aikatar tsare-tsare da raya birane, Misis Adeyanju ta mika takardar murabus din ta sa’o’i bayan da aka mayar da ita wata ma’aikatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/masu-ruwa-da-tsaki-na-apc-kano-sun-nemi-ayi-sulhu-da-yayan-jamiyyar-na-jiha/
A cikin kwafin takardar murabus din ta da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu labari Adeyanju ta yabawa Akeredolu bisa damar da aka ba ta na yiwa al’ummar jihar Ondo hidima.
A cewarta, murabus din na da nasaba ne da wani hukunci na kashin kanta da aka yanke na yin bincike a kan wasu ayyuka a wajen siyasa.
Abin da ke cikin wasikar ya ce, “Na yi murabus daga mukamina na kwamishiniya a Jihar Ondo ba tare da bata lokaci ba.
“Duk da haka, ina godiya a gare ku bisa ga dama ta zinariya da aka ba ni na ba da gudummawa, ci gaban jihar mu, musamman ta hanyar samar da ruwan sha na Kamomi Aketi.
“Kun ba ni dandalin kuma ina alfahari da cewa na yi amfani da shi da kyau don amfanin bil’adama.”
A wani labarin kuma Mai sharhi kan Siyasa Reno Omokri yace ƙasa da mutane 500 suka halarci gangamin yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar Labour Party, gabanin Babban Zaɓen Gwamna na ranar Asabar a Jahar Osun.
Jam’iyar Ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a ranar Laraba ga Lasun Yussuf, Ɗan Takarar Jam’iyyar. Peter Obi ya samu halarta.
A lokacin da yake kira ga ƴan Jahar da kada su saida ƙuri’a, Obi ya shawarce su da u karɓi kuɗi ga Masu sayen ƙuri’u, sannan su zaɓi Jam’iyyar Labour Party.
Yace Yusuf ya cancanta ya zama Gwamnan Jahar Osun na nan gaba.
Da yake maida jawabi, bayan Gangamin yaƙin neman zaɓe, Omokri yace “a takaice mutane da yawa sun halarci gangamin yaƙin neman zaɓe. Idan zagi da gargaɗi za’a maida su ƙuri’u. Oya, ku zageni.
Da yake jawabi ƙarƙashin rubutun sa na Twitter, wani ya rubuta “kai sakarai ne. Babu wani daya tura mutane da yawa.”
“Kai baka tunani zagi, kamar naka, shine dalilin daya sanya ƙasa da mutane 500 suka halarci taron Jam’iyyar ku a Osun? Omokri ya maida jawabi.
A juma’ar data gabata ne, Omokri yace duk abinda ya faru a gareshi to a ɗora laifin ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party.