Masu ruwa da tsakin jam’iyyar SDP sun musanta shigar da Ododo ƙara a Kotu
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Social Democratic Party, SDP a jihar Kogi sun musanta gabatar da kokensu na kalubalantar nasarar zababben gwamnan jihar kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna da aka gudanar a jihar, Ahmed Usman Ododo.
Shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa, Ayo Momodu ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Yayi Sabbin Nadin Mukamai
DAILY POST ta tuna cewa wani rahoto ya fito a ranar Larabar da ta gabata cewa wasu ‘yan bindiga sun sace karar da jam’iyyar SDP ta shigar kan zababben gwamnan a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kogi.
Sakataren Kotun, Mista David Mike, ya yi wannan ikirarin ne bayan da wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ’yan daba ne suka kai masa hari.
Sai dai Ayo Momodu ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa babu irin wannan koke, yana mai cewa ba wani bangare na jam’iyyar da ke kalubalantar zabe a kotu.
“Sakataren kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Kogi ya yi ikirarin cewa an kai masa hari tare da sace koke.
“Bari a fadi gaskiya cewa ba a shigar da kararrakin a gaban Sakatarorin Kotuna ba sai na rajista.
“Muna so mu sake jaddada cewa jam’iyyar SDP ko dan takararta babu wanda ya shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zabe
A wani labarin kuma:Ku ɗauki jindaɗin masu yiwa ƙasa hidima da matukar muhimmanci – DG ga ma’aikatu
Babban Daraktan hukumar masu kula da masu yiwa ƙasa hidima Brigediya Janar Y.D. Ahmed ya bukaci masu daukan ma’aikata da masu ruwa da tsaki da su sanya jindadin masu yiwa ƙasa hidima da aka tura masu domin yin aiki a wuraren su.
DG Ahmed ya yi wannan kiran ne a jiya a lokacin da yake kaddamar da wani kamfani na miliyoyin naira a hukumance a makarantar sakandaren al’umma ta Ihe, karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.