- Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mambobi hudu na majalisar kula da harkokin kasuwanci ta kasa NCP
- Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan
- Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin mambobin majalisar da su kawo mafi kyawun kwarewar kamfanoni masu zaman kansu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mambobi hudu na majalisar kula da harkokin kasuwanci ta kasa (NCP) masu wakiltar kamfanoni masu zaman kansu a majalisar.
Sabbin mambobi hudu sun hada da Oluwole Osin — Kudu maso Yamma, Mohammed Mustapha Bintube — Arewa maso Gabas, Olayiwola Yahaya — Arewa ta Tsakiya da Akwa Effion Okon — Kudu-maso-Kudu.
KARANTA WANNAN: Tsohon Shugaban Kasar Sierra Leone Zai Fuskanci Tambayoyi Kan Yunkurin Juyin Mulki
Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Tinubu ya bukaci sabbin mambobin majalisar da su kawo mafi kyawun kwarewar kamfanoni masu zaman kansu don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun sami kima da tasiri mafi girma daga hannun jarin da aka yi a madadinsu.
A halin da ake ciki, Tinubu ya amince a kwanakin baya cewa Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, zai yi aiki a matsayin Shugaban Hukumar Bunkasa NCDMB ta Najeriya.
Baya ga Lokpobiri, sauran ‘yan Najeriya da aka nada a hukumar sun hada da Engr. Felix Omatsola Ogbe – Babban Sakatare, Oritsemyiwa Eyesan – Mamba / EVP Upstream, NNPCL, Gbenga Komolafe – Mamba / Shugaba, NUPRC, Bekearedebo Augusta Warrens – Mamba, Nicolas Odinuwe – Mamba, Raphael Samuel – Mamba, Sadiq Abubakar – Mamba da Olorundare Sunday Thomas – Memba.
A wani labarin kuma, Hukumar NPC ta Gargadi Jami’anta Game da Magudin Bayanai
Hukumar NPC ta gargadi jami’an da ke da ruwa da tsaki wajen tattara bayanan jama’a na shekarar 2023-2024
NPC tace duk wani nau’i na magudi zai haifar da mummunan sakamako ga jami’an da kuma kasa baki daya
Dole ku Baiwa Ayyukan ku muhimman ci lokacin da kuke Gudanar da Bincike
Hukumar Kidayar jama’a ta Kasa NPC ta gargadi jami’an da ke da ruwa da tsaki wajen tattara bayanai na shekarar 2023-2024, da su tabbatar da sahihancin bayanai daga wadanda suka amsa.
Mista Chidi Ezeoke, kwamishinan tarayya na NPC mai wakiltar jihar Anambra, shine Wanda ya yi wannan gargadin a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Awka.