Fitaccen lauyan kare hakkin dan adam na ƙasar nan, Femi Falana yayi Allah wadai da abun da ya bayyana babban tasirin da dalar Amurka ke da shi a ɓangaren tattiln arzikin Nijeriya, inda ya ƙara da cewa ƙasar nan ba tada wani dalili na sayar da danyen mai a Dalar Amurka. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Babban lauyan yace ya jagoranci wani gangamin akan yaƙi da tasirin da Dalar Amurka ke yiwa tattalin arzikin kasa ga shugabancin babban bankin kasa CBN, inda suka yi alkawarin magance lamarin amma yace sun kasa yin hakan har kawo yanzu.
KU KARANTA: Ku Tuba Ko Ku Fice Daga Jihar Baki Daya — Rundunar Yan sanda Ga Yan bindiga
Falana yayi wannan jawabi a gidan telebijin na Chennels a cikin shirin siyasa mai suna Politics today na ranar Litinin, inda aka tambaye shi akan matsayar Nijeriya dangane da lamarin daya shafi yargeniyar ficewar Birtaniya daga kuñgiyar Tarrayar Turai, da kuma yadda wasu ƙasashe ke ƙoƙarin fitowa da wasu kuɗaɗe na ƙasa da ƙasa domin ƙalubalantar dallar Amurka.
Sai dai ya cacccaki matakin da babban bankin Najeriya ya ɗauka na amincewa da shawarar da asusun bada lamuni na duniya IMF, da kuma bankin duniya, inda yace waɗanan hukumomin sun amince da karya darajar Naira.
Falana ya koka akan yadda ake biyan kudin hayar gidaje da, da kuɗaɗen makaranta da Dalar Amurka a wasu sassan kasar nan.
A wani labarin kuma, Rikicin Cikin Gida: Jam’iyar APC Ta Dakatar Da Mambobinta Guda 14
Jam’iyyar APC reshen Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ta dakatar da wasu mambobinta 14 bisa zarginsu da aikata laifukan da suka shafi cyi wa jam’iyar zagon kasa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun shugaban gundumar Afaka, Mista Auwal Adamu da sakataren jam’iyaf Ismail Yahaya, kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna, ta bayyana cewa kwamitin ya hana su shiga duk wasu harkokin jam’iyyar a shiyyar Afaka da ma jihar Kaduna baki daya.