– Ta ragar-gaza motar Mijinta da duwatsu.
Ta ce ita ce tayi masa ɗanyan aikin ba wani ba – Inji matar da ta farfasa gilashin motar mijin nata.
Wata mata ta lalata motar Mijinta ta hanyar farfasa masa gilasan motar.
Matar wacce wani fefen bidiyo da Jaridar Solacebase ta wallafa a shafin ta na Facebook, ya nuna yadda matar ta farfasa gilasan motar mijin nata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani gwanin ƙira ya samar da dabarar da zata kawo ƙarahen fashin waya.
A lokacin da take wannan ɗanyan aikin, bidiyan ya jiyo matar tana shaidawa mijin nata cewar ita ce take lalata masa motar ba wani ba. Dan haka kada ya zargi kowa.
Da alama shi kansa mijin yana daga sama yana kallon ɗanyen aikin da matar tasa take yi masa.
A duk fasa gilas ɗaya sai ta ɗaga hannu ta nuna shi sannan ta magantu.
Sai dai bai ce komai ba, ya ja bakinsa yayi shuru inda sauran jama’ar dake gurun suka ta kallanta suna mamakin abinda yasa take wannan ragar-gazar motar mijin nata haka.
Bayan ta gama wannan ta’asar, sai kuma ta juyo ta nufo gidanta, in da mai gidan nata yake ciki.
Wannan bidiyan dai ya samu makallata kusan dubu ɗaya da ɗari biyar 1,500, inda kuma da dama suka yaɗa bidiyan.
A WANI LABARIN KUMA: Wata ɗaliba ta ƙunnawa ɗakin kwanan ɗalibai huta, ta kuma ƙi bari a shiga a kashe
Wata ɗaliba a ɗaya daga cikin jami’o’yin dake kasar a dake Abuja, ta bunkawa ɗakin kwanan ɗalibai wuta.
Ɗalibar wacce ta tattaro katifun ɗaliban dake kwana a ɗakin da ta kunnawa wutar ta kuma samo ashana ta kunna huta akan katifun sannan ta fito wajen ɗakin ta tsaya a bakin kofa riƙe da wuƙa a hannunta.
Fefen bidiyan da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna yadda ɗalibar take ta murmushi a lokacin da wutar take ci ta kuma ƙi bari a shiga a kashe wutar.
Bidiyan ya nuna yadda sauran ɗaliban suke ta gudun tsira, sauran kuma na ta kururuwar kawo musu ɗauki duba da yadda hayaƙi ke tashi a sashin kwanan ɗaliban.