Dillalan Shanu Sun Fara Yajin Aiki Kan Neman Diyyar Naira Bilyan N475 da kuma wasu haƙƙoƙin.
Dillalan shanu da na Abinci a karkashin hadaddiyar kungiyar hadahadar abinci da dillancin shanu ta Najeriya (AUFCDN), a yau (Alhamis) za su fara yajin aiki a duk fadin kasar bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da suka ba gwamnatin tarayya domin ta biya bukatunsu.
AUFCDN, wata kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) a ranar Lahadi a wani taron manema labarai ta ce kungiyar na neman kariyar mambobinta ne kawai shi yasa ta Nemi biyan diyyar Naira biliyan 445 na rayukan mambobi da kadarorin da suka yi asara.
Kungiyar kwadagon ta kuma bukaci gwamnati da ta ba da umarnin wargaza duk wasu shingayen da ke kan titunan tarayya saboda matsalolin da mambobinta ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu.