Jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun tarwatsa taron masu zanga-zangar lumana dangane da irin kashe-kashen da ake yi a kudancin Kaduna.
’Yan sandan ɗauke da makamai sun tayar da taron ne a safiyar Asabar kafin masu Zanga-zangar su gama taruwa a mahaɗar Refinery Junction.
Kakakin hukumar ta ’yan sandan jihar, Mohammed Jagile ya ce, “Ba a sanar da mu ba. Mun je mun tarwatsa taron ne saboda haramtacce ne kuma yanzu komai ya lafa.
Ba a samu wata arangama tsakanin ɓangarorin ba duk da cewa da farko ’yan sandan sun kama wasu masu zanga-zangar amma daga baya suka sake su.
Masu zanga-zangar sun fito ne sanye da baƙaƙen kaya dake nuni da halin baƙin ciki da jimami da suke ciki.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-hallaka-mutum-33-a-zangon-katat-na-jihar-kaduna/
Ɗaya daga cikin masu Zanga-zangar da wakilinmu ya samu tattaunawa da shi mai suna Alpha, ya ce sun shirya zanga-zangar bisa lumana domin bayyana damuwarsu ga jama’ar kudancin Kaduna.
“An hana mu gudanar da zanga-zangar domin tun kafin mu taru motoci 15 zuwa 20 na ’yan sanda ɗauke da makamai sun isa wurin.
“Bukatarmu ita ce a samu kwanciyar hankali a kasa. Mun gode Allah komai ya tafi lafiya domin mu da ’yan sandan mun fahimci juna”, cewar Alpha.
Idan ba a manta ba kudancin Kaduna ya daɗe cikin matsalar rashin tsaro, wanda wasu masana harkar tsaro suke ganin cewa gwamnatin jihar da ta tarayya sun gaza wajen kawo ƙarshen matsalar.