Mataimakin Gwamnan Jahar Jigawa, Namadi ya lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna
Mataimakin Gwamnan Jahar Jigawa Malam Umar Namadi ya samu nasarar lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna a Jam’iyyar APC domin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Dayake sanar da Sakamakon zaɓen, Dr. Kabiru Muhammad yace Namadi ya samu nasara bayan ya kada Ƴan Takara 8 daga cikin masu neman kujerar Gwamna da kuri’a 1220.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kula da Haƙƙin Ɗan Adam, tayi Allah wadai da Kisan Harira, ɗiyanta guda 4 a Anambra
A cewar sa, sauran ƴan Takarar sun haɗa da Aminu Kani mai Shekaru 16, da Sanata Sabo Nakudu kuri’a 106, da Farooq Adamu Aliyu da kuri’a 13, da Sani Hussaini Garin-Gabas da kuri’a 5, da kuma Sanata Ibrahim Hassan Hadejia da kuri’a 58.
Ahmad Rufa’i Zakari, da Adamu Mukhtar, da kuma Ahmad Muhammdu basu kuri’a ko ɗaya ba.
A jawabin shi na amincewa, Namadi ya godema Deliget da masu ruwa da tsaki na APC da hukumomin tsaro wajen samun nasarar gudanar zaɓe nagartacce.
Yasha alwashin cigaba da gudanar da kyakkyawan aiki daga inda Gwamna Badaru Abubakar ya tsaya, idan har ya samu nasarar lashe zaben Shekarar 2023.
Comments 1