An Sace Ƴar Takarar Majalisar Jaha ta APC a Jos
Rundunar Ƴan Sandan Jahar Filato a ranar Alhamis ta tabbatar da sace ƴar takarar Majalisar Jaha a ƙarƙashin Jam’iyar APC.
Ƴar Takarar Majalisar Na’anyil Magdalene Dakogol tana neman kujera Majalissa mai Wakiltar Qua’an Pan ta Jahar a Babbar Zaɓen Shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mataimakin Gwamnan Jahar Jigawa, Namadi ya lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Ubah Gabriel Wanda ya tabbatar da garkuwa da’ita a cikin wata sanarwa, yace Kwamishinan Ƴan Sanda ya tura tawagar Ƙwararru domin su ceto ta.
A cewar Madalene an sace ta kwanaki ɗaya kafin gudanar da zaɓen Fidda Gwani.
Sanarwar tace Na’anyil wanda ita kaɗai ce mace mai neman Takarar a APC, tana kan hanyar ta domin haɗawa da Deliget, gabanin gudanar da zaɓen Fidda Gwani.
Comments 1