Mataimakiyar Gwamnan Kaduna ta ziyarci Zangon Kataf, ta yi Allah wadai da kashe-kashe
Biyo bayan kashe-kashen da aka yi a karamar hukumar Zangon Kataf, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a ranar Larabar da ta gabata, ta jagoranci tawagar jami’an gwamnati domin jajantawa al’ummar yankin.
Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, yayin da ta ke yin Allah wadai da kashe-kashen, ta ce sun je ga al’ummar domin isar da ta’aziyyar Gwamna Nasir el-Rufai da daukacin al’ummar jihar ga Agwatyp, HRH Dominic Gambo Yahaya da iyalan wadanda suka rasu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ta Ga Wallen Shi: Budurwa Ta Kunyata Saurayinta a Gaban Mutane, Ta Kwace Kayan Da Ta Siya Masa
A cewarta, gwamnatin jihar ta yi aiki tukuru tare da jami’an tsaro domin bankado wadanda ke da hannu wajen kisan gilla da barnata kaddarori.
A cewar ta, ta umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da ta gudanar da bincike cikin gaggawa tare da bayar da tallafi ga mutanen da lamarin ya shafa.
Da yake mayar da martani, HRH Dominic Gambo Yayaha ya godewa mataimakiyar gwamnan jihar da kuma gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan ziyarar, kamar yadda ya bayyana bakin cikinsa kan munanan hare-haren da ya bayyana a matsayin abin ban tsoro.
Ya kuma koka da cewa harin na zuwa ne bayan wani lokaci na zaman lafiya a cikin kokarin da mutane masu kishin kasa ke yi na inganta zaman lafiya a tsakanin dukkan mutanen da ke zaune a masarautar.
A wani labarin kuma: Ta Ga Wallen Shi: Budurwa Ta Kunyata Saurayinta a Gaban Mutane, Ta Kwace Kayan Da Ta Siya Masa
Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Borno ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa ta amince da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna da za a yi a jihar.
Da yake jawabi a dakin taro na St Patrick Catholic Cathedral ranar Laraba a Maiduguri, shugaban kungiyar CAN na jihar, Most. Rabaran Dr. John Bogna Bakeni, ya yi kira ga masu yada jita-jita da kuma yada jita-jita da su daina yin hakan, yana mai cewa wannan shiri ne na katsalandan da CAN.