Duk da dai mutane na ganin tsara budurwa gaban iyayenta kamar rashin kunya ne, wannan matashin ya gawada yin haka a wannan karon.
Wani matashi kuma mawallafi ya wallafa bidiyon da yayi yayin da yake yi wa mata magana a titi, wanda bidiyon ya yi matukar daukar hankalin jama’a.
KU KARANTA: Matashi ya halaka kishiyar mahaifiyarsa da ‘yarta
A bidiyon, an ga yadda ya do shi wata budurwa wacce ya yi mata magana a gaban iyayenta, Raw nigeria.com ta ruwaito.
Yayin hakan, mahaifiyarta ta yi mamakin irin tsabar kwarin gwiwarsa. Hakan ya sa ta daure fuska yayin da take ba diyarta umarni.
Akwai waka a cikin bidiyon wanda hakan ya hana mutane jin abinda yake cewa. Mahaifin yarinyar ya yi murmushi yayin da yake yi mata magana.
A cikin bidiyon an ga inda matashin ya kawaye budurwar don ya duba ta dakyau.
Wani Matashi Dan Zaman Kashe Wando Ya Rabauta Da Tikitin Zaman Gidan Yari
Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan din Jihar Oyo, a ranar Juma’a ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 32 da haihuwa, Abdullahi Abdulkadiri, wanda ba shi da aikin yi, a gidan yari bisa zargin yunkurin yin fashi da makami.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Abdulkadiri, wanda ba a bayar da adireshin gidansa ba, ana tuhumar sa ne da laifin hada baki da kuma yunkurin yin fashi da makami.