Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta nemi sabbin dabaru don magance matsalolin tsaro da ake fama da su a fadin kasar nan.
A cikin sakonsa na bikiin Ista a ranar Asabar, Mark ya bayyana cewa, koma bayan da aka samu a baya-bayan nan wajen dakile harkokin tsaro ya bukaci sauran masu ruwa da tsaki su gabatar da ra’ayoyinsu kan yadda za a iya magance matsalar.
“Gwamnatin da ke yanzu tana buƙatar buɗe kofofin amsan sabbin dabaru saboda ba ita ce kadai ke da hakkin nemo tsarini ba don nemo hanyoyin magance matsalolinmu. Ba wai batun jam’iyyun siyasa ba ne, addini ko kabilanci ba, amma batun ci gaban al’ummarmu ne.”
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Paul Mumeh, Mark ya fitar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi tunani tare da yin nazari a kan wannan bala’in da ke yanuwa zuwa sassan kasar nan, da nufin sauya munanan matakai domin samun ci gaba, amintacciyar rayuwa da kuma samun rayuwa Mai Ingancin a nan gaba.
“Abin takaici ne ga bil’adama a yi watsi da kalubalen tsaro, ko kuma yin tunanin cewa komai yana da kyau yayin da zamantakewa da siyasar al’umma ta kusan shiga cikin rudani.”
“Ya kamata duk wani mai tunani a cikin al’umma ya damu da halin da al’umma ke ciki tare da karkatar da al’amura ta hanyar da ta dace. Ya kamata mu dakata mu yi tunani a kan halin da al’umma ke ciki, mu nemo hanyar da za a bi a domin warware matsalar a nan gaba.”
“Masu rike da mukamai ya kamata su kasance masu gaskiya su yarda cewa abubuwa ba daidai suke gudana ba, kuma su kasance cikin shiri don jagorantar hanyar samun mafita. Na yi imanin za mu iya sake gyara Najeriya idan muka kuduri aniyar yin aiki tare a cikin yanayin gaskiya da mutunta juna.”
Yayin da yake addu’ar zaman lafiya, sulhu da gafara a cikin ruhun Ista, ya bukaci shugabannin addinai a duk fadin kasar nan, da su yi wa’azin Samar da zaman lafiya, da kuma kulla kyakkyawar alaƙa tsakanin mabiya.
Comments 1