Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Boujee Jessie, ta bayyana yadda matsolon saurayinta yayi kuskuren tura mata kuɗi har sau biyu.
A wani bidiyo da ta sanya ta bayyana cewa matsolon saurayin nata ya tura mata naira dubu ashirin har sau biyu a bisa kuskure. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Allah mai iko: Bidiyon wata ɗaliba mai lallurar makanta mai yin kitso ya ɗauki hankula sosai
Saurayin na ta a cewar ta yayi wannan kuskuren ne a dalilin matsala da ya samu wajen turowa.
Lokacin da ya gano cewa ya tura mata kuɗin har sau biyu, sai yayi gaggawar tura mata saƙo a WhatsApp inda ya gaya mata da dawo masa da naira dubu ashirin ɗin.
Sai dai budurwar, taƙi tura masa. A maimakon hakan sai tace masa bata da kuɗin da za a ɗauka idan ta tura masa.
Saurayin nata yayi ta mata magiya inda yake cewa idan ta dawo masa da kuɗin zai tura mata kuɗin da za a ɗauka idan ta mayar masa da kuɗin.
Daga baya sai ta mayar da martani da wata alamar ɓacewa a WhatsApp sannan ta watsa wa duniya yadda hirar ta su ta kasance a yanar gizo inda ta rubuta:
“Lokacin da matsolon saurayina ya tura min kuɗi har sau biyu bisa kuskure.”
Ta kuma nemi jin ta bakin mutane kan ko ta mayar masa da kuɗin sa ko kuma kada ta mayar masa da su.
Ku kalli bidiyon a nan
Mutane sun tofa albarkacin bakin su sosai a kan bidiyon, ga kaɗan daga cikin waɗanda Ɗimokuradiyya ta tattaro:
@Victor funds ya rubuta:
“Ki mayar masa kada ya zo ya rage miki sadaki.”
@bigmax196 ya rubuta:
“Lol matsolo sannan ya baki kuɗi, me zai hana ki mayar masa da abun sa.”
@Tikis l’amour ta rubuta:
“Ba dai ni ba, ba zan taɓa mayar masa ba.”
@Brown Shuga ta rubuta:
“Lol na taɓa yin irin wannan, a dalilin hakan ya daina yi min magana.”
Cristiano Ronaldo Ya Samu Wani Babban Matsayi a Wasan Da Za Suyi Da Kulob Ɗin Messi
A wani labarin na daban kuma, Cristiano Ronaldo ya samu wani muhimmin matsayi da za suyi da Paris Saint Germain.
Shahararren ɗan wasan ƙwallon kafar nan wato Cristiano Ronaldo, zai jagoranci tawagar zakarun ƴan wasan Saudiyya a fafatawar da za suyi da kulob ɗin PSG, s wani wasan sada zumunta ranar Alhamis, 19 ga watan Janairun 2023.