By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana taya matasan Najeriya murnar zagayowar ranar yara ta duniya 2022.
Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tukuru don ganin kowane yaro ya samu damar yin karatu, wanda hakan zai sa su samu kyakkyawar makoma.
DUBA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: 2023: An Dage Zaben Fidda Gwani Na Jam’iyyar APC A Jihar Oyo
Wata sanarwa a ranar Alhamis ta mai hannun magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, ta ce shugaban Najeriya ya amince da matsayin ilimi a ci gaban kowace kasa.
Gwamnati ta ba da tabbacin cewa Buhari ya himmatu wajen ganin an kara rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Da yake lura da cewa ilimi ya kasance a kan gaba, ya ce sauran batutuwa – kamar su kiwon lafiya, kariya daga cutarwa, kwayoyi, kungiyoyin asiri, fataucin yara da cin zarafi, rikicin cikin gida – suma suna jan hankula.
Buhari ya yi imanin cewa yaran Najeriya sun cancanci mafi kyawu kuma kasa mai aminci inda za su iya girma, yin abokai, mu’amala da tafiye-tafiye cikin ‘yanci, kuma su zama shugabanni masu nasara a fagage daban-daban.
Shugaban ya ce tare da saka hannun jari a ayyukan samar da ababen more rayuwa, ci gaban matasa, ilimi, ICT, tattalin arzikin zamani, al’adu, fasaha da nishaɗi, “muna shimfida tushe ga al’ummomi masu zuwa”.
Comments 1