Yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki garin Geidam, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya janyo tashin hankali a cikin garin.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun durfafi manyan shagunan garin inda suka balle su tare da kwashe kayan abinci da sauran kayan amfani, kafin daga bisani su cinnawa shagunan wuta.
Modu Ali, wani mazaunin garin Geidam ya shaidawa jaridar The Nation cewa ba ya ga shagunan da suka lalata, sun kuma yi awon gaba da kayan abinci.
Ya ce ‘yan ta’addan sun kuma cinnawa gidan Dr. Mulima Mato, tsohon shugaban karamar hukumar wuta.
KARANTA WANNAN: Abun dariya: Bidiyon yadda Obasanjo ke tikar rawa a lokacin motsa jiki
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan snadan jihar ASP Dungus Abdulkarim ya bayyana cewa ‘yan sanda sun gano mota kirar Hilux da aka kona tare da gawarwakin mutane biyu amma ba su tantance ko na mayakan Boko Haram ne ko na mutanen garin ba.
Jami’in ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan cin je har babban asibitin garin inda suka umurci malamar kiwon lafiya da ke aiki a lokacin, da ta duba ‘yan kungiyar da aka jiya ciwo tare da basu magani, kafin suka bar garin.
A cewarsa, ‘yan ta’addar sun yi awon gaba da hakimin Geidam, abunda ake gani da garkuwa da shi.
Gwamna Mai Mala Buni ya umurci hukumar kai daukin gaggawa ta jihar SEMA da ta kai agaji garin Geidam, domin tallafawa wadanda wannan hari ya shafa tare da kuma daukar bayanan ta’asar da suka yi.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya jajantawa al’ummar Geidam bisa wannan harin da ya kira “abun takaici”.
A wani labarin, Al’umma da dama a garin Uba dake karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno sun bace sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka kai a ranar Talata.
Ganau sun shaidawa majiyarmu cewa; Boko Haram din sun kai harin ne da manyan bindigu inda suka zo a Babura da misalin karfe 7:30 na dare, inda suka kwashe kayayyakin abinci a shagunan jama’a kafin daga bisani su cinnawa shagunan wuta.