Mayar da FAAN, CBN: Shettima ya yi jawabi ga masu adawa da matakin Tinubu
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi tsokaci ga masu adawa da matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka na mayar da wasu sassan babban bankin Najeriya CBN da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na tarayyar Najeriya FAAN hedikwatar Abuja zuwa Legas.
Mataimakin shugaban kasar ya ce an dauki wannan mataki ne domin maslaha ga ‘yan Najeriya baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 13 A Hanyar Neja
Shettima, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana haka ne a ranar Asabar a matsayin babban bako na musamman a wajen taron tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara 10 da ya gudana a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Taken taron dai shi ne “Kirkirar Hanyoyi Don Zaman Lafiya: Yaki da ‘Yan Bindiga da Ta’addanci ta hanyar Kyakkyawan Mulki don Ci Gaba Mai Dorewa a Najeriya.”
“Kwanan nan, akwai masu adawa da matakin gwamnatin tarayya kan shirin mayar da wasu ma’aikatu da sassan babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na Najeriya (FAAN) daga Abuja zuwa Legas, ina so na tabbatar wa al’ummar jihar da Arewa cewa matakin an ɗauke shi ne don maslahar ‘yan Najeriya baki daya,” in ji mataimakin shugaban.
Ya ce gwamnati mai ci ba za ta yanke wata manufa ko shawarar da za ta zama bangare ba, ko kuma illa ga wani yanki na kasar.
“Saboda haka, masu adawa da tsarin sauya ma’aikatun na wasu sassan ya kamata su daina, ko kuma suna yin barna,” in ji Shettima.
A wani labarin kuma:AFCON: Kwankwaso, Kanu, da sauransu sun yi tsokaci kan wasan da Najeriya da Kamaru
Tsohon dan wasan Najeriya, Nwankwo Kanu ya taya murna ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles a gasar cin kofin Afrika na 2023, AFCON, a zagaye na 16 wanda ta yi da Kamaru a daren Asabar.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa kwallaye biyun da Ademola Lookman ya ci ne ya baiwa Najeriya nasara akan Indomitable Lions a Ivory Coast.