Wani matashi ɗan Najeriya a shafin Twitter ya bayyana cewa da yawa daga cikin mazajen Najeriya ba su san yadda ake soyayya da mata ba.
Matashin mai suna Uncle Charles a Twitter, wanda ya janyo cece-kuce bayan ya bayyana ra’ayin sa, yace da yawa daga cikin mazaje ƴan Najeriya ba su iya soyayya ba, ga rashin iya sanin yadda za su janyo hankalin matan da abin duniya bai dame su ba. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: “Har yanzu ina ƙaunar su” Cewar matashiyar da ƴan Chana suka sace tana jaririya
Yayi iƙirarin cewa hakan ya sanya suka fi karkata wajen matan da basu da sana’a, saboda sanin cewa za su ruɗe su da abin duniya.
“Mafi yawa daga cikin mazajen Najeriya basu san yadda za suyi soyayya da matan da abin duniya bai ruɗe su ba. Basu lura alamomi, ba su iya nuna shauki da kulawa ba,”
“Kwata-kwata ba su iya soyayya da matan da suka dogara da kan su ba suka tara abin duniya. Wannan shine dalilin da ya sanya suka fi rububi kan matan da ba su da sana’a.” A cewar sa.
Ma’aurata Sun Kai Ƙarar Asibiti Kotu Bayan Sun Musanya Musu Jaririya
A wani labarin na daban kuma, wasu ma’aurata sun garzaya kotu domin neman haƙƙin su bayan wani asibiti ya musanya musu jaririya.
Wasu ma’aurata sun maka wani asibiti a gaban kotu bayan sun gano cewa ba su bane ainihin iyayen ɗiyar su ba.
A cewar wani mai amfani da sunan @Jupinapapi3 a Twitter, mijin yayi gwajin DNA wanda ya tabbatar da cewa ba shine mahaifin yarinyar ba.