Dukkanin alamu sun nuna cewa Lionel Messi zai tsawaita kwantiragin sa da Paris Saint Germain, bayan kakar 2023 dake tafe.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa ɗan wasan baya muradin cigaba da zama a kulob ɗin.
Lionel Messi ya bar Barcelona a shekarar 2021, sannan ya koma PSG a kyauta inda ya haɗu da tsohon abokin sa Neymar.
KU KARANTA KUMA: Abin a yaba: Bidiyon wani ɗan sanda yana ba wani yaro mai taɓin hankali kulawa ya taɓa zuciyoyi
Jaridar Marca ta samo cewa wani ɗan jarida a ƙasar Spain, Gerard Romero, ya rahoto cewa Lionel Messi yana da shakku kan sabunta kwantiragin sa da PSG, inda yake duba yiwuwar zuwa wasu kuloblikan.
“A zuwa yau da muke ciki, niyyar Messi bata tsawaita kwantiragin sa da PSG bace, hakan na nufin ba sabunta kwantiragin sa da PSG.” A cewar Romero.
“Nasarar da ya samu gasar cin kofin duniya ta sauya yadda yake yin tunani, inda yanzu ake ba wasu abubuwan muhimmanci.”
Barcelona yanzu sune waɗanda ake yiwa kallon suna a sahun gaba wajen dawo da Messi.
Sai dai, ɗaya daga cikin sharuɗɗan da zai an cika su kafin Messi ya dawo, shine dole sai ya zaftare wani kaso mai tsoka na albashin sa, domin ba kulob ɗin damar sanya shi cikin kasafin albashin su, saboda halin matsin tattalin arziƙi da suke ciki.
Sauran kuloblukan da suke son kawo Luonel Messi sun haɗa da Inter Miami, Newell’s Old Boys, da Al-Hilal.
An Yiwa Real Madrid Tayin Siyan Babban Ɗan Wasan Paris Saint Germain
A wani labarin na daban kuma an yiwa Real Madrid tayin babban ɗan wasan Paris Saint Germain.
An yiwa Real Madrid tayin wani ciniki wanda suka daɗe suna jiran sa, inda aka ba zakatun na Laliga damar siyan ɗan wasan Paris Saint Germain, Neymar Junior.
Neymar har yanzu shine yake da tarihin zama ɗan wasan da yafi kowane ɗan wasa tsada a duniyar kwallon ƙafa, bayan ya koma Paris Saint Germain daga Barcelona akan kuɗi Yuro miliyan ɗari biyu da ashirin da biyu (€222m) a shekakar 2017.