Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda Lawal, ta yi Allah-wadai da yadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau inda ta bayyana hakan a matsayin rashin imani.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar aiki ga mahukuntan makarantar,inda ta koka da cewa dalibai ba za su iya maida hankali a karkashin wani yanayi na rashin tsaro ba.
Karanta nanZamu Gaggauta Amincewa Da Kasafin Kudin Bana Idan Yazo Hannunmu-Majalisar Wakilai
Uwargidan gwamnan jahar Zamfara ta jajantawa mahukunta, ma’aikata, iyaye, da daukacin daliban jami’ar wadanda aka sace musu yan uwansu.
Ina son in yi muku jaje kan wannan Iftila’in da ya sameku na daukar yan uwanku kuma abokan karatunku da wasu marasa imani sukayi ba tareda laifinsu ba,ku duka ‘ya’yana ne kuma ina ji a jikina cewar daliban da aka sace zassu dawo nan bada jimawa ba.
Gwamnatin da ke karkashin mijina ba ta huta ba a kullum tana sake fasalin gine-ginen tsaro don fatattakar ayyukan ‘yan bindiga daga Jihar inji ta.
A cewarta, hadin gwiwar jami’an tsaro na kan gaba wajen ganin an ceto sauran daliban ba tare da samun wani rauni ba inda kuma ta bada tabbacin cewar da yardar Allah hakann ba zata sake faruwa a jahar ba.
A wani labarin kuma
Gwamna Zulum Ya Bayarda Umarnin Rushe Gidajen Karuwai A Maiduguri
Gwamnan jahar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya bayarda unarnin rushe wasu gine gine da yace karuwai suna cin karensu babu babbaka a wurin gwamnan a wata ziyara daya kai wajen yace ana amfani da kananan yara domin ayi lalata dasu a biyasu,wand hakan babban laifine.