Tun lokacin da wannan hoton wannan ƴar iskar maiyin rawa da hijabi ya bayyana a kafofin sada zumunta, sai ministan ya sha alwashin sai yaga bayan harkar karuwanci da raye-raye na batsa.
Hukumomin garin sun kama ƴan mata da masuyin harka da su da dama, sakamakon wannan namijin ƙoƙarin da ya ɗauka.
Amma a gefe ɗaya akwai masu yin ƙorafi akan wannan matsayi da ministan Abuja ya ɗauka, inda suke cewa ya kamata ministan yasani, Abuja ba birnin Shari’a bane don haka ya kyalesu suyi Shagalin su.