Ministan Abuja Malam Mohammed Musa Bello ya Kira wani taron gaggawa ga jami’an tsaron birnin game da yadda za a kawo karshen sace- sacen mutane a yankin baki daya.
Zaman wanda ya gudana a ranar juma’a ya samu halacin karamar ministar kula da harkokin birnin tarayya Abuja, Dr. Ramatu Tijani Aliyu tare da dukkanin shugabannin hukumomin tsaro dake fadin Abuja.
Kana babban Mai baiwa ministan Abuja shawara kan lamurran tsaro Amsasada Habu Saliu Mohammed da kwamishinan rundunar ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya Babaji Sunday, sun zanta da manema labarai bayan tattaunawar.
Sunday ya bayyana cewa tattaunawar ta tabo abubuwan da suka shafe ayyukan sace _sace, da garkuwa da mutane a yankin babban birnin tarayya Abuja, inda hukumomin tsaro suka bayyana cewa za su yi iya bakin kokarin su wajen ganin abubuwan da ke faruwa ba su ci gaba da faruwa ba.
Kana ya bayyana cewa a yau dukkanin shugabannin hukumomin tsaro za su sake wata tattaunawa a ofishin sa dangane da irin matakan da aka cimma wa a taron gaggawan.
A karshe ya shawararci mazauna babban birnin tarayya da su kula matuka, tare da taimakawa jami’an tsaro da bayanan da suka shafi abubuwan ta’addanci.