Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya isa kasar Mali domin tattaunawa da shugabannin sojojin kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Mista Lavrov, wanda ya ziyarci kasar Iraki a ranar Litinin, inda takwaransa Abdoulaye Diop ya tarbe shi, amma bai fitar da wata sanarwa ba ga manema labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Zamfara ta gargadi CBN, Bankuna kan sabbin takardun kudi
Ana sa ran ministan na Rasha zai tattauna da shugaban rikon kwarya na kasar Assimi Goïta da kuma ministan harkokin wajen kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Rasha Tass ya ce bangarorin biyu za su tattauna batutuwan hadin gwiwa – da suka hada da huldar soji da jigilar hatsi da taki da albarkatun mai na Rasha zuwa kasar Mali.
Tattaunawar za ta kuma tabo batutuwan da suka shafi yakin Ukraine da kuma magance ta’addanci a yankin Sahel.
Wannan shi ne karo na biyu da Mista Lavrov ya kai ziyara Afirka cikin makonni biyu – bayan ya ziyarci Afirka ta Kudu, Angola, Eswatini da kuma Eritrea a watan Janairu.
Tasirin Rasha a Mali na karuwa babu kaukautawa tun bayan tura sojojin haya na Wagner a watan Disamba 2021.
A wani labari kuma, Wata Kotu A Rivers Ta Tasa Keyar Magoya Bayan Atiku Gidan Yari
Wata kotun majistare da ke zamanta a garin Fatakwal a jihar Rivers ta tasa keyar mutane sama da 20 zuwa gidan gyaran hali na jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An kama su ne a wani taro da mambobin kungiyar goyon bayan Atiku a jihar suka yi.