Dan takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar PDP, Sheriff Oborevwori, ya nemi hadin kan ‘yan jarida domin tabbatar da burin mataimakin dan takaran shugaban kasa na Jam’iyar Dokta Arthur Ifeanyi Okowa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Dan majalisar ya yi magana ne a lokacin da ya jawabi a cikin shirin a shirin “Platform”, wani shiri da kungiyar NUJ reshen jihar Delta a Asaba ta shirya domin yiwa yan takara tambayoyi kan manufofin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Zamfara ta gargadi CBN, Bankuna kan sabbin takardun kudi
Oborevwori ya ce, “Zan yi aiki a matsayin gwamnan ga dukan jihar Delta ba tare da la’akari da matsayin a na zamantakewa, addini ko siyasa ba.”
Ya kara da cewa yana da manufa ta musamman da aka tsara don cigaban jihar Delta.
Ya ce, “Ina rokon ku da ku wayar da kan jama’a su zabi dukkannin yan takarar mu na jam’iyar PDP a dukkan matakai wato 5/5″
A wani labari kuma, Ministan Harkokin Wajen Rasha Ya Isa Kasar Mali
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya isa kasar Mali domin tattaunawa da shugabannin sojojin kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Mista Lavrov, wanda ya ziyarci kasar Iraki a ranar Litinin, inda takwaransa Abdoulaye Diop ya tarbe shi, amma bai fitar da wata sanarwa ba ga manema labarai.