Ministan t6saron Najeriya Manjo Janar Salihi Magashi Mai Ritaya ya ce NAjeriya na cikin halin Ha’ula’i biyon kara tabarbarewar harkar tsaro a kasar musamman abin da ya shafi hare-haren ta’addanci da fashin daji da yawan garkuwa da mutane da suka yawaita.
Kazalika ya ce harkar tsaron fah bai ta’allaka kurum akan gwamnati da jami’an tsaro, su ma jama’a da masu ruwa da tsaki akwai irin rawar da za su iya takawa.
Ministan ya yi wannan magana ne a babban taron harkar tsaro da shelkwatar Rundunar Tsaron tarayya a Abuja ya ce dole kowa ya tashi tsaye ya bada gudunmawar shi muddin ana bukatar dakile wadannan matsaloli.