An rantsar da jagoran juyin mulkin sojan kasar Gabon, Janar Brice Nguema a matsayin shugaban Kasar na rikon kwarya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Magoya bayan sabbin shugabannin sojoji sun halarci bikin, yayin da tsofaffin ministocin hambararriyar gwamnatin da suka halarci taron suka yi ta sowa tare da jama’a.
Nguema ya jagoranci juyin mulkin ranar Larabar da ta gabata da ya hambarar da hambararren shugaban Kasar Ali Bongo, jim kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ta takaddama a kai.
Shugaban na rikon kwarya, a cewar BBC, ya shafe mafi yawan aikinsa a matsayin janar na soja a cikin yankin Bongo, har ma an ce dan uwan Ali Bongo ne.
KARANTA WANNAN Sojojin Gabon Sun Bayyana Dalilin Hambarar Da Shugaban Mulkin Dimokuradiyya
Bikin rantsar da shi ya haifar da fargabar cewa watakila ya ci gaba da mulkin Bongo na shekaru 55.
Mahaifin Ali Bongo, Omar, ya yi mulki na tsawon shekaru 41 kafin ya rasu a shekara ta 2009 kuma dansa ya gaje shi.
A wajen bikin rantsar da Nguema, jama’a sun yi ta sowar nuna goyon baya ga sojoji yayin da aka gudanar da fareti a fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar Gabon, wato Libreville.
Bikin rantsar da shi, shi ne na baya-bayan nan a jerin kasashen aka yi wa juyin mulki a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Kasar Gabon dai ita ce kasa ta shida a cikin harshen Faransanci da ta fada karkashin mulkin soja a cikin shekaru ukun da suka gabata a daidai lokacin da tsohuwar mai.yi musu mulkin mallaka Faransa ke fafutukar ganin ta ci gaba da yin tasiri a nahiyar.
An dakatar da Gabon daga kungiyar Tarayyar Afirka bayan juyin mulkin wanda Majalisar Dinkin Duniya da Faransa suka yi Allah wadai da shi.
A Wani Labarin Kuma Sojoji, Da NSCDC Sun Bankado Wasu Wuraren Tace Fetur Ba Bisa Ka’ida Ba
Jami’an rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami’an kula da kadarin Gwamnatin NSCDC sun gano wasu wuraren tace man fetu da ba bisa ka’ida ba a kalla 12.
Sun gano wauraren ne a yankin Owahwa Creek da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.