Moghalu Yayi wani hasashe mai ƙarfi game da Jihohin da kowane Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa zai Lashe
Wani tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar African Democratic Congress, Kingsley Moghalu, ya yi hasashen jihohin da ƴan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu; dana Jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi; da kuma Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, zasu yi nasara sosai.
Moghalu ya yi hasashen cewa Tinubu ne zai samu ƙuri’u mafi rinjaye a jihar Legas, Obi zai samu nasara a jihar Ribas, kuma Kwankwaso ne zai samu mafi yawan kuri’u a jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Wike ya yabawa Buhari kan sakin kason Neja Delta tun 1999
Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, ya ce lamarin ya sa sakamakon zaben 2023 ba shi da tabbas.
A cikin jerin sakonnin Twitter, Moghalu ya ce babu wanda zai iya hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.
A cewarsa, abu ne mai kyau ‘yan siyasa su yi gumi don neman kuri’u a 2023.
Ya rubuta: “Ina hasashen @KwankwasoRM zai lashe mafi yawan kuri’un Kano a zaben shugaban kasa. @officialABAT zai yi nasara a Legas, kuma @PeterObi zai yi nasara a Rivers.
“Jahohi uku daga cikin hudu mafi yawan jama’a a Najeriya. Wannan yanayin ya sa sakamakon zaben bai da tabbas.
“Duk wanda ya gaya maka wanda zai ci zaben shugaban kasa “tabbas” yana yaudarar ku – ko watakila kansa ko kanta.
“Wannan abu ne mai kyau ga dimokradiyya. A bar ‘yan siyasa su yi gumi. Mu dai muna fatan su yi gumin mulki kamar yadda suke zufa domin su ci nasara.
“Akwai sauran jahohin da ke da yawan kuri’u irin su Oyo ma (duk da cewa gwamnatin PDP ba ta tare da Atiku a halin yanzu). Kaduna da Katsina, duk da cewa dukkansu jihohin APC ne masu karfi. Amma ba za mu taɓa sanin abin da zai faru da gaske ba.
A wani labarin kuma: Abin da Peter Obi yake yi bayan duk tafiyar sa – Aisha Yesufu
Shahararriyar ‘yar fafutuka, Aisha Yesufu ta bayyana cewa Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, yakan bukaci tawagarsa da ta binciki ayyukansa bayan kowane fita waje da kuma nuna masa kura-kurai.
A cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na twitter a daren Juma’a, mai goyon bayan Obi ta ce dan takarar LP mutum ne da ke son koyo.