Rundunar atisayen Hadarin Daji ne suka ‘yanto daliban makarantar Sakandaren gwamnati dake Kankara a jihar Katsina, kamar yadda John Enenche, Daraktan yada labarai na Hedikwatar tsaron Nijeriya ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Inda ya ce sun cika alkawarin da suka dauka na dawo da daliban cikin koshin lafiya wanda adadinsu ya kai 344 a ranar Alhamis din 17 ga watan Disambar 2020.
Ya kara da cewa sun samu nasarar ‘yanto ne sakamakon bayanan sirri da rundunar sojin ta yi amfani da su, inda suka nuna kwarewa wajen ganin an dawo da su da rayukansu.
A karshe Hedikwatar tsaron ta jinjinawa rundunar Hadarin Daji da sauran hukumomin tsaro wajen wannan aikin tare da sauran al’umma da suka bayar da bayanai na musamman da suka taimaka wajen ‘yanto daliban.