By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon shugaban Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Rimingado, ya sake samun ‘yanci tare da cika sharuddan belinsa.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Mista Rimingado ya sake haduwa da iyalansa a gidansa da ke titin Yahaya Gusau.
DUBA WANNAN LABARIN: Kwara: ‘Yan Sanda Sun Cafko Mutane 3 Da Ake Zargin Barayi Ne, Da Wasu 2 Masu Karbar Kayan Sata A Ilorin
Wata kotun majistare da ke Kano karkashin jagorancin babban Alkali Aminu Gabari a ranar Juma’a ta bayar da belin Mista Rimingado bayan gurfanar dashi karo na farko.
A ranar Alhamis ne ‘yan sanda dauke da makamai suka kama tsohon shugaban PCACC a masaukin Gwamnan Sokoto da ke Abuja, inda ya je tantance shi a matsayin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP.
An tattaro cewa ‘yan sandan sun tafi da shi nan da nan bayan an tantance shi inda suka kai shi ofishin babban birnin tarayya Abuja, daga bisani kuma suka tuso keyar sa zuwa Kano domin fuskantar tuhuma.
An tuhumi Mista Rimingado ne da laifin yada bayanan karya, sabanin sashe na 149 na dokar shari’a ta shekarar 2019.
Sai dai tsohon shugaban Hukumar Muhuyi Rimingado Ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Da yake yanke hukunci kan neman belin, Mista Gabari ya bayar da belin Muhuyi Rimingado a kan kudi Naira 500,000 tare da wasu amintattun mutane biyu wadanda za su kasance mahaifin sa, ko kanin mahaifin sa da kuma ba wa kotu izinin biyan haraji na shekaru uku.
Hakazalika kotun ta umarci wanda ake kara ya kawo babban limamin masallacin Juma’a na Sharada, ko kuma shugaban kauyen Sharada Dagaci a matsayin wani bangare na sharudan belin.
Kotun ta kuma umurci Mista Rimingado da ya ajiye fasfo dinsa na kasa da kasa zuwa wurin rajistar kotun domin mika shi zuwa ofishin babban magatakardar jihar Kano.
Comments 1