Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kano a Jam’iyyar PDP Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya Jajantawa Al’ummar Jahar Kano, da na Sabongari musamman waɗanda Fashewar Tukunyar Gas ya shafa a Kano.
Wannan na Ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Taimaka mashi akan Kafafen Yaɗa Labaru dasu zama masu haƙuri a lokacin da suke fita zuwa gudanar da harkokin su na yau da Kullum.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DUMI-DUMI: An dakatar da Akanta Janar na kasa, har sai baba ta gani, kan zargin badakalar Naira 80
Barista Magaji yayi nuni dacewa irin muhimmiyar rawar da Kano ke takawa wajen cigaban harkokin Najeriya bazai iya misaltuwa ba, sakamakon ƙabilu da dama a Jahar.
Yayi kira ga Kowa da ya cigaba da Addu’o’i domin samun zaman lafiya da lumana a Jahar, a yayinda aka tunkari Babban Zaɓen.
Jigo a Jam’iyyar PDP yace Fashewar Tukunyar Gas babban abune da ya cancanci zubar da hawaye, saboda Al’umma su cigaba da haɗa kansu, a yayinda aka haɗa hannu domin ciyar da Jahar Kano a matakin gaba.
Magaji ya kuma yi kira ga kowa da kowa daya guji yaɗa labarun ƙarya akan lamarin koda Fashewar Tukunyar Gas ne ko kuma Fashewar Bom.
Ya kuma yi ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ƴan uwansu sakamakon wannan mummunan lamari, tare da yin addu’a ga Allah daya sanya wannan shine na ƙarshe da zai faru anan gaba.