Jam’iyyar APC Mai Mulki ta kasa ta tsayar da sabon ranar da za ta gudanar da zaben shugaban kasa da sauran dukkanin zabukan fidda gwani.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar Felix Morka.
Sanarwar mai taken, ‘APC ta daidaita jadawalin ayyukan zaben fidda gwani na shekarar 2023’.
Kana sanarwar ta ce, kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa ya amince da sabbin ranakun gudanar da zaben fidda gwani a taron da ta yi a ranar Laraba.
Morka ya ce za a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa ne a ranar 29 ga Mayu, 2022.
Sanarwar ta ce, “Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar APC a ranar Laraba, 18 ga Mayu, 2022, ya amince da daidaita jadawalin zabukan fidda gwani na Gwamna, Majalisar Dokokin Jiha, Majalisar Wakilai, Majalisar Dattawa da na Shugaban kasa da kuma shigar da kararrakin zabe.:
“zamukan yan Majalisar Wakilai -zai gudana ne a ranar Alhamis, 26 ga Mayu, 2022.
“Majalisar Dattijai da Majalisar – Juma’a, 27 ga Mayu, 2022.
“Don kararrakin zabe: Gwamna da Majalisar Wakilai – Juma’a, 27 ga Mayu, 2022.
“Majalisar Dattijai zai guda na ne a ranar – Asabar, 28 ga Mayu, 2022.
Taron na musamman don zaben fidda gwani na shugaban kasa zai gudana ne a ranar Lahadi 29 ga wata, da kuma ranar Litinin, 30 ga Mayu shekarar 2022.