By Abbas Yakubu Yaura
Mukaddashin Alkalin Alkalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga, ya rantsar da sabbin alkalai 24 da hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar (JSC) ta amince da su.
A cewarsa, tara daga cikinsu an nada su a matsayin manyan alkalan kotunan majistare ta II tare da wasu 15 a matsayin alkalan kotuna ta daya I.
Pindiga ya tunatar da sabbin alkalan da aka rantsar da su gudanar da adalci ga kowadanne irin mutane ba tare da la’akari da asalinsu, akida da addininsu ba.
Mukaddashin alkalin alkalan ya bukace su da su kasance masu bin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 yayin da suke gudanar da ayyukansu, inda ya bukace su dasu dinga mika kararrakin su a kowannen wata zuwa ga mataimakin magatakarda domin tantance ayyukansu.
Pindiga ya kuma yi kira ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ya kammala aikin ginin rukunin kotunan Majistare da ke cikin birnin Gombe domin saukaka wahalhalun da alkalai ke fuskanta na raba kotuna.