Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta ce ta kammala shirin kakabawa mambobinta da ke Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Owerri, FUTO da Mataimakin Shugaban Jami’ar takunkumi kan “ba bisa ka’ida ba” da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Dr. Isa Ali Pantami.
Kungiyar wadda ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da shugabanta na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ya gudanar a Legas a ranar Litinin, ta ce kara girman ministar ga Farfesa ya sabawa doka.
A cewar kungiyar ASUU, ba zai taba yiwuwa a zama minista da malami a lokaci guda ba, inda suka bayyana karin girma a matsayin wacce aka bayar ta haramtacciyar hanya.
Kungiyar ta bai wa Pantami zabin yin murabus daga mukaminsa na minista, inda ta ce a halin yanzu bai cancanci a dauke shi a matsayin Farfesa ba.