Mutum ashirin ne suka mutu sakamakon hatsarin da wata motar fasinja ta yi, kamar yadda kafar watsa labaran kasar Aljeriya ta labarto a ranar Juma’a.
Hatsarin har wala yau ya jikkata mutum 11. Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne a Kudancin garin Tamanrasset a ranar Alhamis. Mafi yawan wadanda hatsarin ya rutsa da su ‘yan Afrika ne.
Har yanzu ba a tantance mene ne ya haifar da hatsarin ba.