Gwamnatin Jahar Katsina ta sanar da kulle Asusun Bankuna 232 data gada daga Gwamnatin data gabata ta Jam’iyyar PDP a Shekarar 2015, tare da samo Naira Biliyan 4 a cikin su.
Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Hon. Faruk Lawal Jobe ya bayyana haka ga Manema Labaru, jim kaɗan bayan ya bayyana aniyar sa ta Son tsayawa Takarar Gwamnan Jahar Katsina a Shekarar 2023 a Jahar.
Wasu Matasa a ƙarƙashin Ƙungiyar Nigerian Youths Congress suka yi taro da Jobe inda suka bashi takarda, suna kira a gareshi daya fito Takarar Gwamnan Jahar Katsina a Shekarar 2023, akan abinda suka bayyana cewa dabarun sa sun inganta kuɗaɗen shiga a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NSCDC ta Musanta rahoton Hana bin wasu hanyoyi a jihar Kebbi Saboda Yan bindiga
Jobe yace Gwamnatin Shema ta Jam’iyyar PDP ta miƙa wa Gwamna Aminu Bello Masari Asusu 29 a Shekarar 2015, amma bayan an gudanar da bincike mai zurfi, an gano ƙarin wasu Asusu 232, kuma kuɗaɗen dake ciki sun kai Naira Biliyan 4.
Ya ƙara dacewa, Gwamnatin Jahar ta rufe Asusun, kuma kuɗaɗen ciki an cire su, kuma aka tura su ga Asusun Kuɗaɗen Shiga na Gwamnati domin shimfiɗa ayyukan cigaba a Jahar.
Yace “aikina na farko a lokacin dana zama Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman ta Fuskar Bankuna da Kuɗi, shine na kulle Asusu 232 na Ma’aikatu da Sassa-sassa da Hukumomin Gwamnati na Jahar Katsina, wanda ba’a gaya mana dasu ba a lokacin da muka karɓi Mulki a Shekarar 2015.
“Kuma kuɗaɗen dake ciki na waɗannan Asusu 232 shine Biliyan 4. Babu rahoton waɗannan Asusai a lokacin da aka bamu Gwamnati. Takardun da aka miƙa ma wannan Gwamnati Mulki a Shekarar 2015 shine akwai Asusu 29.”
Ya ƙara dacewa a matsayin sa na Baiwa Gwamna Shawara akan Banki da kuɗi, na samu nasarar toshe dukkanin wasu ɓaraka, rage kuɗaɗen da ake kashewa, tare da ɓullo da ingantattun hanyoyin samu kuɗaɗen shiga a Jahar.
Ya bayyana cewar, idan aka zaɓe shi a Matsayin Gwamnan Jahar Katsina a Shekarar 2023, zai tunkari ɓullo da shirye-shiryen tallafawa Matasa, da shirye-shiryen Koyon Sana’o’i, da magance zaman kashe wando da rage rashin ayyukan yi a Jahar.