Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga hannun Akanta-Janar na kasa, Idris Ahmed da aka dakatar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani na Ministoci da kungiyar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: ICPC Ta Gurfanar Da Wani Ma’aikacin Gwamnati A Gaban Kuliya Bisa Tuhumar Sa Da Karban Kudade Da Jabun Takardu
A yanzu haka dai hukumar tana tuhumar Akanta Janar na kasa da aka dakatar bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.
Shugaban EFCC, wanda ya nuna nasarorin da hukumar ta samu daga watan Janairu zuwa Disamba, 2022, ya bayyana wasu abubuwan da suka kwato kamar N134,33,759,574.25, $121,769,076.30, £21,020.00, €156,925.00, ¥21,000.00 CFA.00 da dai sauransu.
Bawa, wanda ya ci gaba da magana kan ayyukan da hukumar ta yi zuwa yanzu a karkashin sa, ya ce hukumar EFCC ba ta ja da baya a kan zargin damfarar Naira biliyan 7.1 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Abia kuma Mai tsawatarwa na majalissar, Sanata Orji Uzor Kalu.
A wani labari kuma, Majalissar Wakilai Ta Sauya Ranar Da Gwamnan CBN Zai Gurfana A Gabanta
Majalisar wakilai ta dageranar da gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele zai bayyana a gabatan har zuwa mako mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An sake dage zaman ne ranar Alhamis bayan Emefiele ya sanar da ‘yan majalisar cewa ya yi tafiya tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Washington.
Idan dai za a iya tunawa an bukaci Emefiele da ya gurfana a gaban majalisar domin yin bayani kan sabuwar manufar kayyade cire kudi a banki.
Mataimakin kakakin majalisar Idris Wase wanda ya jagoranci zaman na ranar Alhamis ne ya karanta wasikar Emefiele.